Isa ga babban shafi

Rasha ta sake bude ofishin jakadanci a Burkina Faso bayan shekaru 32 da kullewa

Rasha ta sake bude ofishin jakadancinta a birnin Ouagadagou na Burkina Faso shekaru 32 bayan kullewa a 1992, matakin da ke nuna dawowar kakkarfar alaka tsakanin kasar ta tsohuwar tarayyar Soviet da kuma kasar ta Sahel.

Shugaba Vladimir Putin na Rasha tare da shugaban mulkin Sojin Burkina Faso kyaftin Ibrahim Traore.
Shugaba Vladimir Putin na Rasha tare da shugaban mulkin Sojin Burkina Faso kyaftin Ibrahim Traore. AP - Sergei Bobylev
Talla

Wata sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen Burkina Faso ta fitar ne, ke tabbatar da wannan mataki a yau Alhamis, haka zalika jakadan Rasha a Ivory Coast Alexei Saltykov ya tabbatar da matakin inda ya ce kowanne lokaci daga yanzu shugaba Vladimir Putin zai sanar da jakadan da Moscow za ta aika Ouagadougou.

Saltykov ya bayyana cewa kafin aiko da sabon jakadan, shi da kansa zai jagoranci Ofishin jakadancin na Rasha a Ouagadougou daga yau Alhamis.

Tun a shekarar 1992 ne, Rasha ta kulle ofishin jakadancinta da ke Burkina Faso, sai dai bayan sanarwar budewar a yau, Rashan ta bayyana kasar a matsayin babbar kawa kuma tsohuwar abokiyar hulda.

Burkina Faso wadda a bara ta fuskanci juyin mulkin Soji har sau biyu wadanda dukkaninsu ake alakantawa da tabarbarewar tsaro a baya-bayan nan kasar na nuna bukatar komawa hulda da Rasha.

Tun bayan hawansa mulki a watan Satumban 2022 kyaftin Ibrahim Traore ya fara nesanta Burkina Faso da Faransa wadda ta yi musu mulkin mallaka tare da komawa kawance da Rasha.

Ko a watan Oktoban da ya gabata, sai da Burkina Faso ta kulla wata yarjejeniyar ginin tashar makamashin nukiliya don wadata kasar da lantarki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.