Isa ga babban shafi

Burkina Faso ta tilasta wani tsohon minista shiga aikin Soji bayan sukar Sojoji

Gwamnatin Sojin Burkina Faso ta tisa keyar Ablassé Ouedraogo, tsohon ministan wajen kasar kuma jagoran jam’iyyar adawa ta Le Faso Autre zuwa fagen daaga don taimakawa a yaki da ‘yan ta’addan da suka addabi kasar ta yankin Sahel matakin da ke zuwa bayan sukar da ya yi kan cewa Sojin kasar ba su shirya kawar da matsalar tsaro ba.

Jagoran mulkin Sojin Burkina Faso kyaftin Ibrahim Traore.
Jagoran mulkin Sojin Burkina Faso kyaftin Ibrahim Traore. REUTERS - VINCENT BADO
Talla

Wasu ganau sun shaida cewa da misalin karfe 6:30 na yammacin ranar Lahadi ne wasu motocin Sojin Burkina Faso suka yi dirar mikiya a kofar gidan Ablasse Ouedraogo da ke yankin Ouaga tare da tisa keyarsa wanda daga nan kuma aka kai shi fagen dagar don yaki da 'yan ta'adda.

Rahotanni sun ce kamen jagoran jam’iyyar adawar kuma tsohon ministan wajen na Burkina Faso na zuwa ne kwanaki kalilan bayan dawowarsa daga dogon balaguron da ya yi a ketare kuma a dai dai lokacin ya ke tarbar baki masu yi misa barka da dawowa.

Ablassé Ouedraogo mai shekaru 70 wanda ya jima yana sukar salon kamun ludayin Sojojin da suka kwace iko da mulkin Burkina Faso a baya-bayan nan ne ya yi wasu kalamai da ke cewa Sojin kasar ba da gaske suke ba a yakin da suke da ‘yan ta’adda, kalaman da ake ganin sun fusata gwamnatin kasar.

Karkashin dokokin Burkina Faso dai gwamnati na iya tilastawa al’umma shiga aikin Soji, kuma tun gabanin dawowar Ablasse Ouedraogo gida a karshen makon jiya, tuni gwamnatin mulkin Sojin kasar karkashin jagorancin Kyaftin Ibrahim Traore ta fitar da sunansa a cikin jerin wadanda sabuwar dokar tilasta aikin Soja za ta aiki akansu, dalilin da ya sanya tisa keyarsa zuwa bakin daaga.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.