Isa ga babban shafi

MDD ta bukaci bincike kan mutuwar wasu manyan 'yan adawa 10 a Libya

Ofishin majalisar dinkin duniya a Libya, ya bukaci gwamnatin kasar ta tabbatar da gudanar da bincike kan mutuwar mutane 10 ciki kuwa har da tsohon minista Al-Mahdi Al-Barghathi a hannun gwamnatin daya bangaren.

Khalifa Hafter pda 'yan adawa ke masa kallon dan mulkin kama karya a Libya.
Khalifa Hafter pda 'yan adawa ke masa kallon dan mulkin kama karya a Libya. AFP/File
Talla

Majalisar dinkin duniyar ta ce ta damu matuka da mutuwar mutanen a hannun ‘yan adawa sakamakon zargin azabtarwa tun bayan da aka kama su a ranar 7 ga watan Octoban bara.

kamen nasu ya zo ne bayan da rikici ya tashi tsakanin gwamnatocin biyu wato wadanda ke samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya da kuma masu goyon bayan Khalifa Haftar.

Har yanzu dai babu wasu cikakkun bayanai kan yadda aka yi mutanen suka mutu, sai dai yanayin gawarwakin su sun nuna cewa azabtar da su aka yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.