Isa ga babban shafi

Togo ta sanya watan Afrilu don gudanar da zaben 'yan majalisu da na yanki

A ranar 13 ga watan Afrilu ne za a gudanar da zaben 'yan majalisar dokoki da na yanki a Togo, kamar yadda gwamnatin kasar ta sanar a jiya Alhamis a gidan talabijin na kasar.Shugaba Faure Gnassingbe ya sha alwashin gudanar da zabe cikin watanni 12 sama da shekara guda da ta gabata.

Shugaban kasar Togo Faure Gnassingbé.
Shugaban kasar Togo Faure Gnassingbé. © Gnassingbe Twitter
Talla

An gudanar da zaben ‘yan Majalisu  na karshe a kasar ta Togo a shekarar 2018, zaben da ‘yan adawa suka kaurace wa, wadanda suka yi tir da rashin bin ka’ida a lokacin zaben.'Yan adawa na fatan a wannan karon za su kalubalanci jam'iyyar Union for the Republic (UNIR) mai mulki tare da yin kira da a gudanar da rajistar.

Jean-Pierre Fabre, daya daga cikin yan siysasar kasar Togo
Jean-Pierre Fabre, daya daga cikin yan siysasar kasar Togo AFP - PIUS UTOMI EKPEI

 

Yawa Kouigan, ministan sadarwa, ya ce bisa ga ka'idar zabe da jadawalin da hukumar zabe mai zaman kanta ta gabatar, za a gudanar da zaben ranar Asabar 13 ga Afrilu, 2024. Za a gudanar da yakin neman zaben ne daga ranar 28 ga Maris zuwa 11 ga Afrilu. Kamar yadda aka yi a zabukan baya, jami’an tsaro za su kada kuri’a sa’o’i 72 kafin zaben,domin ba su damar samar da tsaro a ranar zabe.

 

Shugaban kasar Togo Faure Gnassingbé.
Shugaban kasar Togo Faure Gnassingbé. © Gnassingbe Twitter

 

A watan Janairu 2024, Majalisar Dokokin Togo ta yi gyare-gyaren wata doka da ta kara yawan mataimakan wadannan zabukan ‘yan majalisar daga 91 zuwa 113. Shugaba Gnassingbe ya hau karagar mulki a shekara ta 2005 bayan rasuwar mahaifinsa Janar Gnassingbe Eyadéma wanda ya shafe shekaru 38 yana mulkin Togo. Tuni dai aka sake zabensa sau uku.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.