Kungiyar kare 'Yan Jaridu ta (CPJ) ta yi kira da a sako 'yan jaridu a Togo
A kasar Togo, Kungiyar kare 'Yan Jaridu ta (CPJ) ta yi kira da a sako Loïc Lawson, darektan jaridar Le Flambeau des Démocrates, da Anani Sossou, dan jarida mai rubutun ra'ayin ta hanyar yanar gizo, da ake tsare da su a gidan yarin Lome babban birnin kasar tun ranar 15 ga watan Nuwamban nan.
Wallafawa ranar:
‘Yan jaridan biyu dai na fuskantar tuhuma biyo bayan shigar da kara da Ministan tsare-tsare na Birane, Adedzé Kodjo ya yi kan zargin bata masa suna.
Wadanan yan jarida a shafukan sada zumunta sun ambaci cewa, an sace kudin CFA miliyan 400 daga wani gida na wannan Minista.
Da gidan rediyo RFI ya tuntubi Jonathan Rozen, babban jami’in bincike a kungiyar kare ‘yan jarida (CPJ), ya yi la’akari da cewa Togo na bukatar sake duba dokokinta, domin a cewarsa aikin jarida ba laifi ba ne.
"Halin da ake ciki yana da damuwa kuma ya cancanci kulawar mu, musamman tun da CPJ ta ba da kyautar 'yancin 'yan jarida ta kasa da kasa ga dan jaridar Togo Ferdinand Ayité.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu