Isa ga babban shafi

Togo ta daure manyan sojojinta shekaru 20 a gidan yari

An yanke wa wasu hafsoshinn sojin Togo hukuncin zaman gidan yari daga shekaru 5 zuwa 20, bayan da aka same su da hannu a kisan wani hafsan soji mai mukamin kanar, Bitala Madjoulba, wanda ke da kusanci da shugaba Faure Gnassingbé a shekarar 2020. 

Wata tawagar sojojin Togo a bakin aiki.
Wata tawagar sojojin Togo a bakin aiki. AFP - PIUS UTOMI EKPEI
Talla

 

Sojoji 7 ne aka gurfanar gaban kuliya daga ranar 23 ga watan Oktoba, inda ake zargin su da laifin hadin baki wajen aikata kisa da ma kisan kansa, da kuma yunkurin yi wa  tsarin shari’a da tsaron kasar zagon-kasa. 

Daga cikin wadanda aka yanke wa hukuncin, akwai  Manjo Janar Abalo Kadangha, tsohon babban hafsan hafsoshi na sojin kasar, wanda zai yi zaman kaso na shekaru 20 a maimakon 50 da mai gabatar da kara ya bukata. 

An sami gawar Laftanar Kanar Bitala Madjoulba,  wanda ya jagoranci rundunar kai daukin gaggawa mai kunshe da dakaru na musamman a ofishinsa da ke wani sansanin soji a ranar 4 ga  watan Mayun shekarar 2020, kwana guda bayan rantsar da shugaba Faure Gnassingbe, don yin wa’adi na 4 a kan karagar mulkin Togo. 

Gwajin da aka yi a kan gawarsa, ya nuna cewa hafsan sojin mai shekaru 51, kuma mai matukar goyon bayan Gnassingbe, wanda dakarunsa suka murkushe jerin zanga-zanga masu muni da aka yi a kasar a shekarun 2017 da 2018 ya mutu ne sakamakon raunukan harbin bindiga. 

An karbe matsayin hafsoshin da aka yanke wa wannan hukuncin, kana kotu ta umurce su su biya kasar diyyar Yuro miliyan daya da rabi  a kan barnar da suka yi mata

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.