ECOWAS ta bukaci maido da tsohon jadawalin zaben kasar Senegal
Kungiyar ECOWAS, ta bukaci gwamnatin Senegal ta gaggauta maido da tsohon jadawalin zaben shugabancin kasar da ta sauya, bayan da ta dage gudanarsa daga watan Fabarairu zuwa karshen wannan shekara.
Wallafawa ranar:
Cikin sanarwar da ta fitar, kungiyar kasashen ta yammacin Afrika ta ce tana bin dukkanin abubuwan da ke faruwa a Senegal sau da kafa, bayan zanga-zangar adawar da ta rikide zuwa tarzoma saboda dage babban zaben da aka tsara yi daga ranar 25 ga watan Fabrairu zuwa 15 ga watan Disamba.
A daren ranar Litinin, Majalisar dokokin kasar Senegal ta kada kuri'ar tabbatar da daukar matakin, tare da bai wa shugaba Macky Sall damar ci gaba da zama kan karagar mulki har sai an nada wanda zai gaje shi.
Wannan ce ta sa a jiya Talata ‘yan adawa suka kamanta dage zaben shugabancin na Senegal da juyin mulki, rashin tabbatas din da suka ce shi ne mafi muni da al’ummar kasar suka gani a siyasance cikin gwamman shekaru.
Senegal dai ba ta taba fuskantar juyin mulki ba tun bayan samun 'yancin kai daga Faransa a shekara ta 1960, abinda ya sa ake mata kallon zama abin misali a bin tsarin mulkin dimokaradiya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu