Isa ga babban shafi

Karim Wade ya samu cikakkiyar damar tsayawa takara a zaben Senegal

An kawo karshen takaddamar da ke neman hana Karim Wade damar tsayawa takara a zaben Senegal, bayan da Faransa ta amince da soke kasancewarsa mai rike da shaidar zama dan kasar.

Dimbin magoya bayan Karim Wade a Senegal.
Dimbin magoya bayan Karim Wade a Senegal. © AFP
Talla

Karkashin dokokin Senegal, babu wanda zai iya tsayawa takarar neman kujerar shugaban kasa idan har ya na rike da shaidar kasancewa dan wata kasa daban duk kuwa da kasancewarshi cikakken dan Senegal.

Wade wanda ya ke shirin yiwa jam’iyyar PDS takara don neman kujerar shugaban kasa a babban zaben da ke tafe cikin wannan shekarar, shugaba Emmanuel Macron da kansa ya samar da wata doka wadda Firaminista Gabriel Attal ya sanyawa hannu da ta bayar da damar cire Wade daga matsayin mai rike da shaidar zama Bafaranshe.

Wannan mataki na Faransa dai na zuwa ne kwanaki kalilan gabanin karewar wa’adin tattara sunayen ‘yan takarar da za su fafata a zaben shugaban kasar.

Tun farko Thierno Alassane Sall ne ya kalubalanci takarar Karim Wade bisa cewa ya na rike da shaidar kasancewa Bafaranshe batun da ya haddasa cece-kuce tare da fargabar Wade ya rasa damar.

Karkashin dokokin Senegal dole dan takara ya kasance cikakken dan Senegal ba tare da mallakar shaidar wata kas aba, haka zalika dole shekarunsa su kasance daga 35 zuwa 75 gabanin iya tsayawa takarar shugaban kasa.

Wade mai shekaru 55 da ya shafe shekaru 3 a gidan yari gabanin yi masa afuwa na sahun ‘yan takarar da ke da dimbin magoya baya a Senegal.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.