Isa ga babban shafi

Sall ya sanar da dage zaben shugaban kasar Senegal na wannan watan

Afirka – Shugaban kasar Senegal Macky Sall ya sanar da dage zaben shugaban kasar da aka shirya gudanarwa a ranar 25 ga wannan wata na Fabarairu, sa’oi kafin kaddamar da yakin neman zaben da aka shirya yi gobe lahadi.

Shugaban kasa Macky Sall lokacin da yake jawabi ga jama'ar kasar yau asabar
Shugaban kasa Macky Sall lokacin da yake jawabi ga jama'ar kasar yau asabar © Capture d'écran Facebook / Macky Sall
Talla

A jawabin da ya yiwa jama’ar kasar, shugaban yace ya dauki matakin rattaba hannu a kan dokar dage zaben domin bai wa ‘yan majalisu damar gudanar da bincike a kan wasu manyan alkalan kotun kundin tsarin mulki guda 2 da ake zargi da aikata ba dai dai ba.

Jiya juma’a ministar kula da ci gaban al’umma, Theresa Faye ta bayyana goyan bayan ta na jinkirta zaben na akalla watanni 6 domin bada damar kammala binciken na majalisa.

Karim Wade da Khalifa Sall da Ousmane Sonko
Karim Wade da Khalifa Sall da Ousmane Sonko © FMM

A watan jiya kotun fasalta kundin tsarin mulkin ta amince da ‘yan takara guda 20 domin tsayawa takarar zaben, yayin da ta soke takarar wasu da dama cikin su harda shugabannin ‘yan adawa Ousmane Sonko da Karim Wade.

A larabar da ta gabata, gwamnatin Senegal ta amince da kwamitin binciken da zai yi nazari a kan ayyukan kotun fasalta kundin tsarin mulkin, kotun dake tantance ‘yan takarar zaben shugaban kasa da kuma tabbatar da wanda ya samu nasara.

‘Yan majalisu da dama daga jam’iyyar dake mulkin kasar sun goyi bayan gudanar da binciken, abinda ya kai ga zargin su da yunkurin jinkirta zaben.

Wade da kotun ta haramtawa shiga takarar zabe ya bukaci gudanar da bincike a kan rawar da alkalan suka taka, inda ya zargi 2 daga cikin su da alaka da wasu ‘yan takarar cikin su harda firaminista Amadou Ba wanda ake zargin cewar shugaban kasa mai barin gado Macky Sall na mara masa baya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.