Isa ga babban shafi

Kotun Ghana ta yi wa wasu mutum 12 daurin rai da rai kan kisan Soja

Babbar kotun Ghana ta aike da wasu mutane 12 gidan yari na tsawon rayuwarsu  sakamakon samunsu da laifin kisan wani Sojan kasar Major Maxwell Mahama shekaru 7 da suka gabata.

Hoton gudumar Alkali.
Hoton gudumar Alkali. © african-court.org
Talla

Kotun wadda ke zamanta a birnin Accra fadar gwamnatin kasar ta samu mutanen 12 da laifin yin tarayya wajen kisan Major Mahama a yankin Denkyira Obuasi cikin watan Mayun shekarar 2017.

Cikin mutanen da za su fuskanci wannan dauri na rai da rai akwai wani dan siyasa wanda shi ne ya tunzura jama’a wajen aikata kisan, yayinda wasu mutum biyu kuma aka sallame su bayan wankesu daga aikata laifin.

Major Mahama mai shekaru 32 ya gamu da ajalinsa ne bayan da mutanen suka farmake shi bisa zargin kasancewarsa dan fashi da makami, duk kuwa da cewa ya na cikin jami’an da ke bayar da tsaro a wata mahaka da ke yankin.

Kisan na Major Mahama ya haddasa tashe-tashen hankula da ya kai ga kamen fiye da mutane 50 da ake zargi da hannu a ta’annatin yayinda aka gurfanar da wasu 14 cikinsu 12 suka fuskanci hukuncin na daurin rai da rai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.