Isa ga babban shafi

Na yafe wa dan majalisar Ghana da ya mini shagube - Maguire

Dan wasan bayan Manchester United, Harry Maguire, ya amince ya yafe wa wani dan majalisar dokokin kasar Ghana da ya yi masa shagube yayin zaman majalisar a shekarar bara.

Dan wasan bayan Manchester United kenan, Harry Maguire.
Dan wasan bayan Manchester United kenan, Harry Maguire. AFP
Talla

Dan wasan wanda ya wallafa a shafinsa na X Wanda aka fi sani da Twitter, ya ajiye wa dan majalisar sakon cewa sai mun hadu a filin wasa na Old Trafford.

Shi dai Isaac Adongo a yayin zaman mahawara kan kasafin kudin kasar da aka gudanar a shekarara 2022, an jiyo yana kalamai marasa dadi ga Maguire, inda yake danganta koma bayan tattalin arzikin kasar da ake samu da irin rawar da dan wasan ke takawa a Manchester United.

Sai dai kuma, a ranar Talata aka sake jiyo shi wannan dan majalisa na neman afuwar Maguire, inda har ma ya bayyana shi a matsayin zakakurin dan wasa da ke bayar da gudun mowa ainun don ganin cewa kungiyar ta kai ga gaci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.