Isa ga babban shafi

Birtaniya na shirin mayar da kayan tarihin masarautar Ashanti, da aka wawashe shekaru 150 baya

Birtaniya na shirin mayar da kayan tarihi kusan abubuwa talatin da aka sace a lokacin mulkin mallaka zuwa Ghana. Gidan adana kayan tarihi na Victoria da Albert da gidan tarihi na Biritaniya ne suka bayyana cimma yarjejeniyar mayar da kayan tarihin masarautar Ashanti, da aka wawashe shekaru 150 da suka wuce, sun koma Ghana.

Kayan gidan tarihi na gidan sarauta na Uni
Kayan gidan tarihi na gidan sarauta na Uni AP - Dominic Naish
Talla

A wannan yarjejeniya ,birnin Kumasi na Ghana zai iya rike waɗannan kayan tarihi talatin na tsawon shekaru uku, yarjejeniyar da za a sabunta sau daya.

A hukumance ,Ghana ta yi magana game da wata taska ta ƙasa da ke shirin komawa ƙasar: kwatankwacin kambin Jewels na masarautar Ashanti, wanda sojojin mulkin mallaka suka kwashe wadannan kayan tarihi talatin. Akwai takobin biki, kayan ado, da kayan kwalliya.

 

Wasu daga cikin kayan tarihi na kasar Ghana
Wasu daga cikin kayan tarihi na kasar Ghana © Victoria and Albert Museum, Lo - Naish, Dominic (Photographer)

Kusan dukkan abubuwa an yi su ne da zinariya ko azurfa. Sojojin Burtaniya ne suka sace su a karni na 19 kuma an baje su a gidajen tarihi guda biyu na Landan, Gidan Tarihi na Biritaniya.

 

 

Wasu daga cikin kayan tarihi a gidan tarihi na Touluse
Wasu daga cikin kayan tarihi a gidan tarihi na Touluse Musee d'Histoire Naturelle de Toulouse/AFP

Kusan dukkan abubuwa an yi su ne da zinariya ko azurfa. Sojojin Burtaniya ne suka sace su a karni na 19 kuma an baje su a gidajen tarihi guda biyu na Landan, Gidan Tarihi na Biritaniya.

Wani al’amari da ke tayar da hankali shine cewa Birtaniya na da hanyoyin da za ta adana wadanan kayan tarihi,sai dai  ƙasashe kamar su Ghana da suka fito ba za su ba da wadanan wurare da suka dace.

Baya ga kasar ta Ghana,akwai kasashe kamar Najeriya da ke neman a dawo da tagulla na kasar Benin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.