Isa ga babban shafi

Gwamnatin Ghana na shirin karkatar da akalar bautar kasa zuwa bada horo kan aikin gona

Gwamnatin kasar Ghana da hadin gwiwar wasu kamfanoni na cikin gida da na kasashen ketare zasu horas da matasa dubu 90 aikin gona, karkashin tsarin bautar kasa da ke zama tilas ga duk dalibin da ya gama jami’a.

Wani manomi yana shayar da gonarsa a Ghana.
Wani manomi yana shayar da gonarsa a Ghana. © Flickr.com CC BY NC ND 2.0 Nana kofi acquah / IWMI
Talla

Tuni dai gwamnati ta rattaba hannu kan yarjejeniyar kusan dala miliyan 12 da kamfanin Agri-Impac Group don gudanar da wannan aiki.

Yarjejeniyar ta kunshi takaita wannan tsarin ga wasu yankunan kasar na shekaru hudu, kafin daga bisani a fadada shi, da zarar an ga nasarar aikin.

Wannan dai na cikin hanyoyin da gwamnatin Nana Akufo Addo ke bi wajen kawo karshen zaman kashe wando musamman a tsakanin matasa, da kuma shafe hanyar habbaka tattalin arzikin kasar ta hanyar noma.

Bayanai na nuna cewa za’a fi mayar da hankali wajen koyawa matasan fasahar noman tumatir, waken suya da kuma kiwon kaji, wanda zai samar da guraben aiki dubu 316.

Ana sa ran baiwa matasan horo, ta yadda zasu horas da daliban kwalejojin Ilimi da na fasaha, abinda ke nufin akwai kwarin gwiwar horon zai isa ga matasan da ke bukatar ya jewa cikin dan kankanin lokaci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.