Isa ga babban shafi

Sojin Somalia sun fara kokarin kwato jirgin MDD da Al Shabab ta kwace

Rundunar Sojin Somalia ta fara wani yunkuri don kwato jirgin jami’an Majalisar Dinkin Duniya da mayakan Al-Shabab suka kwace a jiya bayan fadowar jirgin a yankin da ke karkashin ikon mayakan wanda ya kai ga kisan mutum guda cikin jami’ai 5 da ke ciki, yayinda suka kame sauran shidan da ke ciki ko da ya ke 2 sun yi nasarar tserewa.

Wasu dakarun Sojin Somalia a birnin Mogadishu.
Wasu dakarun Sojin Somalia a birnin Mogadishu. AP - Farah Abdi Warsameh
Talla

A cewar rundunar Sojin ta Somalia, dakarunta sun bazu a gab da yankin da abin ya faru don laluben jirgin da kuma kubutar da mutanen da ke tsare a hannun mayakan na Al-Shabab.

Rahotanni sun ce jirgin ya gamu da tangardar farfela wanda ya kai shi ga fadowa a yankin na Al-shabab, kungiyar da ta shafe shekaru ta na yaki da Somalia har ma da sojojin ketare da ke taimakawa a yakin.

Jirgin na Majalisar Dinkin Duniya kirar shalkwafta na kan hanyar kai daukin gaggawa ne lokacin da matsalar ta faru.

Majiyar Majalisar ta ce cikin mutane 9 da ke cikin jirgin akwai guda dan Somalia yayinda sauran jami’an lafiya na kasashen Afrika.

Tuni dai Majalisar dinkin duniyar ta ce dukkanin mutanen ba jami’anta ne na dindindin ba domin kuwa suna aiki ne na wucin gadi don kai dauki Somalia.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.