Isa ga babban shafi

Ya kamata a fara jefe masu luwadi - Shugaban Burundi

Shugaban Burundi, Evariste Ndayishimiye, ya bayar da shawarar cewa ya kamata a fara jefe masu aikata laifin auren jinsi a gaban taron jama’a

Shugaban Burundi, Evariste Ndayishimiye, lokacin da yake gabatar da jawabi a taron COP27 ranar 8 ga Nuwamba, 2022, a kasar Masar.
Shugaban Burundi, Evariste Ndayishimiye, lokacin da yake gabatar da jawabi a taron COP27 ranar 8 ga Nuwamba, 2022, a kasar Masar. AP - Peter Dejong
Talla

Evariste Ndayishimiye, ya kuma caccaki kasashen Yammacin duniya, kan yadda suke matsawa kasashen da ke kyamar auren jinsi lamba.

Tun a shekarar 2009 aka kafa dokar yanke zaman shekaru biyu a gidan yari ga duk wandda aka samu da laifin aikata luwadi ko kuma auren jinsi a Burundi, kasar da ta kasance mai tsatssauran ra’ayin addinin kirista a gabashin Afirka.

Ndayishimiye, wanda ya kasance mabiyin darikar Katolika, ya ce auren jinsi haramun ne a addinin kiristancci kuma abin kyama ga al’adun kasar.

“Ni dai a ganina, idan muka samu irin wadannan mutane da aikata auren jinsi ko kuma luwadi, to kuwa babu abin da ya kamace su, shine a samu babban filin taro a ajiye su, tare da kiran taron jama’a domin jefe su,” in ji Ndayishimiye.

Ya kuma yi tir da yadda kasashen Yamma ke matsawa kananan kasashe ala tilas sai ssun halasta auren jinsi ko kuma a ddaina basu taimakon jin kai.

Ya ce, ‘yan Burundi da ke rayuwa a kasashen waje, wadanda suka rungumi akidar auren jinsi su ci gaba da zama a can, ba sai sun koma kasar ba.

Auren jinsi dai haramun ne a kasashen gabashin Afirka dda dama, wadanda ke da tarihin nuna kyama ga masu aikata hakan, da kuma nuna musu kyama, musamman wadanda suka rungumi koyarwar addinin musulunci ko kuma kiristanci.

A watan Mayu ne, kasar Uganda, ta ayyana hukunci mai tsauri ga duk wanda aka samu da aikata auren jinsi, abin da ya fuskanci suka ddaga kasashen yammaci da kungiyoyinsu.

Hakan ta sanya a wancan lokaci, Amurka ta ce za ta cire kasar Uganda daga ccikin kasashen da take huldar kasuwanci da ssu, tare da haramta bayar da bisa shiga kasar ga manyan jami’anta, inda bankin bayar da lamuni na duniya, IMF ya dakatar da sabon Shirin bayar da bashi ga kasar.

A watan Maris din wannan shekarar ne, Burundi ta yanke wa mutum 24 hukuncin zaman gidan yari, bayan samunsu da laifin auren jinsi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.