Isa ga babban shafi

Akufo-Addo ya bukaci hadin kan Afirka don neman diyya daga masu mulkin mallaka

Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo ya bukaci shugabannin kasashen Afirka da a hada kai kan bukatar neman diyya daga turawan mulkin mallaka kan barnar da suka yi a zamanin mulkin mallakar. 

Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo. 23/09/21
Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo. 23/09/21 AP - Jacquelyn Martin
Talla

Akufo Ado wanda ke zantawa da wasu shugabannin Afirka a Accra babban birinin kasar, ya ce babu kudi da zai iya biyan abin da ‘yan mulkin mallaka suka yi, masamman cikinkin bayi, amma ya zama dole masu mulkin mallaka su san akwai bashi a kansu. 

A baya-bayan nan dai wasu shugabannin kasashen Yammacin Turai sun fara amincewa lallai an tafka kurakurani a zamanin mulkin mallaka a Afirka, inda gidajen tarihi suka fara mayar da dukiyoyi da kayayyakin tarihi da aka sace a Afirka. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.