Isa ga babban shafi

Sojojin gwamnatin Habasha sun sake kwace ikon birnin Lalibela

Birnin Lalibela a yankin arewa na kasar Habasha, daya daga cikin birane dake kumshe da mujamiu ya koma hannun dakarun Gwamnati, rahotanni daga yankin na bayyana cewa mayakan sa kai da aka sani da sunan "Fano' sun fice daga garin cikin dare vayan mamaye gari na wani lokaci.

Un milicien Afar à Shewa Robit, en Ethiopie, en décembre 2021.
Un milicien Afar à Shewa Robit, en Ethiopie, en décembre 2021. AFP - AMANUEL SILESHI
Talla

A baya dai mayakan sa kai  sun goyi bayan sojojin Habasha tsawon shekaru biyu na rikici tsakaninta da hukumomin 'yan tawaye na yankin Tigray, wanda ya kare tare da yarjejeniyar da aka sanya hannu a watan Nuwamba 2022 a Pretoria na kasar Afirka ta Kudu.

Sai bai da dama na kallon wannan yarjejeniya a matsayin koma baya ga kawance yayin da 'yan kabilar Amhara ke zaman doya da man ja da mutanen Tigray.

Wasu daga cikin mutanen  yankin Guyah, mai nisan kilometa 100 km da Semera.
Wasu daga cikin mutanen yankin Guyah, mai nisan kilometa 100 km da Semera. AFP - MICHELE SPATARI

Yarjejeniyar ta kara dagula al'amura a yankin na Amhara, Wanda ya kawo cikas ga tsarin hukumomin a bangaren da ya shafi  yunkurin kwance damarar sojojin yankin a watan Afrilu.

Tsawon wani lokaci kafin wayewar gari,mayaka yan sa kai da aka sani da  Fano ne ke rike da mafi yawan garuruwan, sun hada karfi da sauren mayaka wajen barin garin,” in ji wani mazaunin garin wanda shi ma ya nemi a sakaya sunansa saboda dalilan tsaro.

Map of the Amhara and Tigray region in Ethiopia
Map of the Amhara and Tigray region in Ethiopia © AFP

A ranar Laraba da yamma wasu mazauna yankin sun nuna cewa mayakan sa kai na kungiyar Fano ne ke iko da mafi yawan Lalibela kuma an sake tura dakarun gwamnatin tarayya zuwa wajen wani sansani da ke gefen garin.

Kasa ta biyu mafi yawan jama'a a Afirka da kusan mutane  miliyan 120, Habasha, kasa da kusan kabilu  80, ta shiga rikici wanda ya daidaita kasar da kuma haifar da yan gudun hijira da dama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.