Isa ga babban shafi

EU ta kulla yarjejeniyar kawance da Habasha karon farko bayan rikicin Tigray

Gwamnatin Habasha da kungiyar Tarayyar Turai sun sanya hannu kan wata sabuwar yarjejeniyar kawance mai kunshe da tallafin tsabar kudi yuro miliyan 650, karon farko da wata yarjejeniya ke shiga tsakanin bangarorin biyu, tun bayan samun baraka a tsakaninsu shekaru 2 da suka gabata.

Firaministan Habasha, Abiy Ahmed.
Firaministan Habasha, Abiy Ahmed. AP - Mulugeta Ayene
Talla

Yayin wani taro tsakanin ministan kudi na Habasha Ahmed Side da shugabar sashen kula da kawancen kungiyar EU Jutta Urpilainen ne aka kai ga cimma yarjejeniyar taimakekeniyar junan mai kunshe da tsabar kudi yuro miliyan 650.  

Jutta Urpilainen a jawabin da ta gabatar gaban taron na birnin Addis Ababa ta ce lokaci ya yi daya kamata, bangarorin biyu su dawo da alakar da ke tsakaninsu bayan da mahukuntan Habasha suka amince da matakin tsagaita wuta a rikicin da ke faruwa a yankin Tigray tun cikin watan Nuwamban bara.

Kunshin kudin dai wani bangare ne na tallafin yuro biliyan guda da EU za ta baiwa Habasha tsakanin shekarar 2021 zuwa 2027 amma kuma aka dakatar tun bayan barkewar yakin na yankin Tigray a shekarar 2020.

Firaminista Abiy Ahmed na Habasha Wanda ya yi maraba da kunshin tallafin, ya bayyana cewa tallafin na EU zai taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin kasar da ke farfadowa daga yaki kuma take bukatar garambawul ga bangaren tattalin arziki.

A cewar Abiy Ahmed, yarjejeniyar kawance da fahimtar juna ta fara dawowa kan turba tsakanin bangarorin biyu.

A ziyarar ta Urpilainen a Habasha, ta samu ganawa da Firaministan baya ga shugaban kungiyar Afrika Moussa Faki Mahamat.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.