Isa ga babban shafi

Sojojin Saudiya sun kashe dubban 'yan ci-ranin Habasha - HRW

Kungiyar Kare Hakkin Dan Adam ta Human Rights Watch ta zargi dakarun da ke aikin tsare iyakar kasar Saudiya da bude wa 'yan ci-ranin kasar Habasha wuta, inda suka kashe dubbai tun daga shekarar bara. 

Wani jam'in tsaron Saudiyya kenan akan iyakar kasar
Wani jam'in tsaron Saudiyya kenan akan iyakar kasar AFP - FAYEZ NURELDINE
Talla

Bayanai sun ce mafi yawan ‘yan ci-ranin na yunkurin shiga Saudiya ne daga kasar Yemen, bayan da suka tserewa yaki daga kasarsu.

Kunigiyar ta Human Rights watch ta ce ta gano tare da tabbatar da faruwar kisan bayan binciken karkashin kasa da ta gudanar, inda ta ce wannan  kisan abin takaici ne, kuma wannan zai iya kara yawan tashin hankalin da ke faruwa a kasashen kuryar gabashin Afrika.

HRW ta ce wata matashiya ‘yar shekara 20 da ta tattauna da ita, ta tabbatar mata da cewa dakarun iyakar Saudiyar sun bude musu wuta a lokacin da suke yunkurin shiga kasar, jim kadan bayan sakin su daga gidan yari da mahukuntan Yemen suka yi, tana mai cewa da kyar ta tsira.

Ta ce,

Muna cikin tafiya kawai sai muka ji sun bude mana wuta tamkar ruwan sama, haka muka tarwaste, wasu na gudu wasu suka kwanta, yayin da muke ta kuka kuma a take wasu suka mutu”

Matashiyar ta kuma kara da cewa

Har yanzu idan na rufe idanuna ina hango wani matashi da harbin ya tsinke masa kafafuwansa biyu, yana ta ihu yana cewa yanzu haka za ku tafi ku barni? don Allah kar ku tafi ku barni a nan, amma haka muka gudu don ba za mu iya ceton sa ba”

Ko da take karin haske Shugabar Sashen Bincike ta Kungiyar, Nadia Hardman ta ce wannan rashin Imani ne kuma abin takaici ne da kungiyar ba za ta amince da shi ba.

Sai dai kuma ko da Kamfanin Dillancin Labaran Faransa AFP ya tuntubi mahukuntan Saudiya, sun musanta zargin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.