Isa ga babban shafi
Ghislaine Dupont da Claude Verlon

'Yan jaridar Congo da Benin sun lashe kyautar RFI ta 2023

Ɗan jaridar Congo Joseph Kahongo da Ange Joël Agbla Injiniya daga jamhuriyar Benin sun lashe kyautar RFI ta Ghislaine Dupont da Claude Verlon ta 2023. 

Ange Joël Agbla et Joseph Kahongo entourés de la PDG de France Médias Monde Marie-Christine Saragosse et du directeur de RFI Jean-Marc Four.
Ange Joël Agbla et Joseph Kahongo entourés de la PDG de France Médias Monde Marie-Christine Saragosse et du directeur de RFI Jean-Marc Four. © RFI
Talla

An karrama matasan biyu ne wannan Alhamis, yayin wani katsaitaccen buki da aka gudanar a birnin Abijan na kasar Cote d'Ivoire, wanda ke matsayin martaba ‘yan jaridan RFI biyu Ghislaine Dupont da Claude Verlon da aka yi wa kissan gilla a kidal na kasar Mali yayin gudanar da aikinsu a 2013. 

Wanene Joseph Kahongo?

Joseph Kahongo, mai shekaru 27, dan asalin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo, ya yi digirin digirgir a fannin aikin jarida a Jami'ar Lubumbashi, a halin yanzu dan jarida ne, mai gabatarwa a gidan rediyo da talabijin na Malaika, a birnin Lubumbashi. 

Joseph Kahongo.
Joseph Kahongo. © RFI/Ladili

Alkalai sun zabe shi ne amatsayin wanda ya yi nasara cikin ‘yan takara da dama, kan rahoton da ya gabatar  game da wani nauyin abin maye da ake kira "Gaddafi cocktails", wanda ke neman zama ruwan dare tsakanin matasan kasar. 

Ange Joël Agbla

Shi kuwa Ange Joël Agbla, mai shekaru 23, dan kasar Benin ne. Ya yi karatunsa a  Jami'ar Abomey-Calavi, tare da samun horo kan hada sautuka da rahotanni a cibiyoyi da dama ciki harda CFH Production, da kuma gidan Rediyo da Talabijin na Benin (ORTB). A halin yanzu shi ma'aikaci ne a gidan Rediyon Univer da ke Abomey-Calavi.

Injiniyan sauti dan kasar Benin Ange Joël Agbla da ya lashe kyautar RFI tare da Jean-Marc Four, shugaban RFI. 02/11/23
Injiniyan sauti dan kasar Benin Ange Joël Agbla da ya lashe kyautar RFI tare da Jean-Marc Four, shugaban RFI. 02/11/23 © RFI/Ladili

 Ya hada rahoto ne mai kyakkyawan sautuka ta yadda mai sauroro zai fahimci sanar kiwon kaji, inda ya leka wata gonar kaji da kuma yanayin aiki tafiyar da al’amuran. 

Kyautar Ghislaine Dupont da Claude Verlon

An ɓullo da shirin ba da lambar yabon ne, don karrama ‘yan jaridar RFI biyu Ghislaine Dupont da Claude Verlon da aka yi wa kisan gilla shekaru 10 da suka gabata yayin da suke gudanar da aikinsu na jarida a kasar Mali. 

Gasar karo na goma an bude wa kasashen Afirka 25 masu magana da harshen Faransanci, a bana an shirya bukin a kasar Ivory Coast.  

Takara

Fiye da ‘yan takara 330 a bangaren ‘yan jarida da injiniyoyin sautuka suka shiga gasar ta wannan shekara, kafin aka tankade aka zaɓi ƙwararrun matasa 20; ‘Yan jaridu 10 da masu hada hada sautuka 10 daga ƙasashe 12. Dukkansu sun ci gajiyar horo a harabar gidan rediyon RTI (Radiodiffusion Télévision ivoirienne) sun kwashe makonni biyu suna samun horo daga, shugaban horo na RFI Rachel Locatelli, da Muriel Pomponne, ɗan jarida a RFI kuma babban editan harsunan ketare. 

A karshen horon, an bukaci 'yan takarar 'yan jarida su samar da rahoto mai taken "Tattaunawa da haƙuri" yayin da 'yan takara masu fasaha suka shirya rahoto kan tattalin arzikin Ivory Coast. 

Kuna iya latsa alamar sauti domin sauraren Jean-Marc Four, Shugaban RFI kuma jagoran alkalan da suka tantance nasarar matasan biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.