Isa ga babban shafi

Lafiyar jagoran adawar Senegal na cikin hadari saboda yajin cin abinci

Jagoran ‘yan adawa a Senegal Ousmane Sonko da ake tsare da shi, wanda kwanaki 8 da suka wuce ya koma yajin cin abinci ya samu nakasu a lafiyarsa, kuma yana bangaren kula da marasa lafiya da ke halin rai-kwakwai-mutu-kwakwai, kamar yadda daya daga cikin lauyoyinsa ya bayyana a Larabar nan. 

Ousame Sonko dai ya dage kan cewa tilas sai kotu ta sake shi
Ousame Sonko dai ya dage kan cewa tilas sai kotu ta sake shi AFP - KIRAN RIDLEY
Talla

Sonko ya fita daga hayyacinsa na dan gajeren lokaci a ranar 23 ga wannan watan Oktoba, a cewar lauya Cire Cledor Ly, inda ya kara da cewa ya samu damar ganawa da shi kwana guda kafin ranar. 

Sonko, wanda ya kudiri aniyar tsayawa takarar shugabancin Senegal a zaben watan Fabrairu mai zuwa, ya zargi shugaba Macky Sall da amfani da matakan shari’a ba bisa ka’ida ba wajen taka masa birki a fagen siyasa, zargin da Sally a musanta. 

Sonko dai ya fada rikici da gwamnatin kasar ne tun bayan da ya nuna sha’awarsa ta tsayawa takara a zaben 2024, abinda ya danganta da yunkurin hana shi takara ta kowanne irin hali, zargin da gwamnatin ta musanta.

Shi kansa shugaba Macky Sall yana cikin masu sha’awar tsayawa takara a karo na uku, bayan ya shafe shekaru 7 yanzu haka akan karaga.

A yanzu haka dai Sonko yana zaman kaso ne bayan hukuncin daurin shekaru 2 da kotu ta yanke masa sakamakon samun sa da laifin yunkurin lalata da kananan yara, zargin da ya sha musantawa, tare da ikirarin an kakaba masa ne kawai don hana shi takara da gangan.

Idan har ta tabbata Sonko ya shafe shekaru 2 da aka yanke masa, wannan ya na nufin ba zai tsaya takara ba, matakin da yake tsananin adawa da shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.