Isa ga babban shafi

MDD da AU sun bukaci kwantar da hankula kan rikicin Senegal

Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar Tarayyar Afirka sun yi kira da a kwantar da hankula a kasar Senegal bayan barkewar wani kazamin rikici da ya kai ga hukumomi baza sojoji.

Jami'an tsaron Senegal a lokacin zanga-zanar adawa da tsare Sonko 1/06/23
Jami'an tsaron Senegal a lokacin zanga-zanar adawa da tsare Sonko 1/06/23 REUTERS - ZOHRA BENSEMRA
Talla

Akalla mutane tara aka kashe tun ranar Alhamis sakamakon rikici da ya barke bayan yanke wa fitaccen dan adawar kasar, Ousmane Sonko, hukuncin daurin shekaru biyu a gidan yari, matakin da ka iya fitar hana shi takarar a zaben shugaban kasar na 2024.

Sabon rikici

Ko a jiya Jumma an kashe mutum guda a wani sabon rikici da ya barke a yankin Casamance da ke kudancin kasar lokacin da masu zanga-zangar suka kai hari ofishin ‘yan sanda, kamar yadda kakakin gwamnati ya shaidawa gidan talabijin na TFM.

Sakatare-janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi Allah-wadai da tashin hankalin, inda ya yi kira ga bangarorin ke da hannu a rikicin da su yi taka tsan-tsan.

AU

Kungiyar Tarayyar Afirka ta ce shugaban hukumar gudanarwarta Moussa Faki Mahamat, ya yi kakkausar suka kan rikicin, ya kuma bukaci shugabannin da su guji duk wani mataki da zai lalata dimokuradiyyar Senegal, wadda a ko da yaushe Afirka ke alfahari da ita.

Kungiyar kasashen yammacin Afirka (ECOWAS) ta yi kira ga dukkan bangarorin da su kare martabar kasar da ake yabo a matsayin tushen zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Faransa

Ita ma kungiyar EU masamman Faransa da ta yi wa  mulkin mallaka ta nuna damuwa kan tashe tashen hankular.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.