Isa ga babban shafi

Ana neman dakushe fatan Sanko na neman shugabancin kasar Senegal

Wata kotu a kasar Senegal ta yankewa madugun adawa Ousmane Sonko hukuncin daurin talala na watanni shida a wata shari’ar kan bata suna da ka iya kawo masa cikas ga takararsa ta shugaban kasa a zaben shekara mai zuwa.

Madugun Adawar Senegal Ousmane SONKO
Madugun Adawar Senegal Ousmane SONKO © RFI
Talla

 

Sonko ya zo na uku a zaben shugaban kasa na shekarar 2019 kuma yana da niyyar sake tsayawa takara a 2024, amma shari’o’i biyu da ake masa na iya lalata masa lissafi.

Kotun farko ta yanke masa hukuncin daurin talala na watanni biyu ne da tara mai tsoka a cikin watan Maris saboda bata sunan ministan yawon bude ido Mame Mbaye Niang, hukucin da kotun daukaka kara a Dakar ta kara zuwa watanni shida a ranar Litinin, lamarin da ka iya sanya Sonko shiga jerin wadanda basu cancanci shiga takara ba.

Baboucar Cisse, lauyan ministan, ya shaidawa manema labarai cewa hukuncin zai kawar da Sonko daga zaben shugaban kasa a 2024 idan har aka tabbatar da shi bayan wa'adin kwanaki shida na daukaka kara.

Kotun ta kuma umarci Sonko ya biya CFA miliyan 200 (kimanin dala 330,000) a matsayin diyya ga Niang.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.