Isa ga babban shafi
Senegal

Mutane 4 sun mutu yayin arangama tsakanin 'yan sanda da magoya bayan Sonko

An ci gaba ta tashin hankali a kasar Sengal, yayin da hukumomin suka lashi takobin yin amfani da “duk hanyoyin da suka dace” wajen dawo da doka da oda, bayan arangamar da ya barke tsakanin ‘yan sanda da magoya bayan jagoran adawar kasar Ousmane Sonko, inda Ministan cikin gida ya ce mutane hudu suka mutu yanzu haka biyo bayan rikicin.

Motar jami'an tsaro a Senehgal yayin da ya isa inda magoya bayan madugun adawar kasar  Ousmane Sonko, a Dakar, ranar 5 ga watab Maris 2021.
Motar jami'an tsaro a Senehgal yayin da ya isa inda magoya bayan madugun adawar kasar Ousmane Sonko, a Dakar, ranar 5 ga watab Maris 2021. REUTERS - ZOHRA BENSEMRA
Talla

Rikicin ya biyo bayan hukuncin da wata kotu ta yanke na ci gaba da tsare madugun adawar Ousmane Sonko da ake zargi da laifin aikata Fyade.

Tuni Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bukaci dukkan bangarorin da su kauce wa tada hankali.

Mai magana da yawunsa Stephane Dujarric ya fadawa manema labarai a New York cewa "Dole ne zanga-zangar ta kasance cikin lumana, kuma dole ne jami'an tsaro da na 'yan sanda a kowane lokaci su yi aiki ... daidai da ka'idojin kare hakkin dan adam na duniya."

Kama Ousman Sonko

Yanzu haka jaoran adawar kasar ya shafe daren farko a kukuku, tun bayan da jami’an tsaro a Senegal suka kame shi a birnin Dakar biyo bayan arrangamar da aka yi tsakanin jami’an tsaron da wasu magoya bayansa.

A lokacin da Sonko mai shekaru 46 ke kan hanyar zuwa kotu domin fuskantar tuhumar da ake masa kan laifin fyade ne aka baiwa hammata iska tsakanin wasu daruruwan magoya bayansa da ke masa rakiya da jami’an tsaro, wadanda suka afka wa ta hanyar jifa da duwatsu, abin da ya sa su kuma maida martani da barkonon tsohuwa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.