Isa ga babban shafi

Kotun ICC ta janye tuhumar da take yi wa madugun 'yan tawayen Anti-Balaka

Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya ICC ta janye daukacin tuhume-tuhumen da take yi wa tsohon madugun ‘yan tawayen Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya, Maxime Makom a wannan Alhamis. 

Madugun 'yan tawayen Anti-Balaka na Afrika ta Tsakiya Maxime Mokom.
Madugun 'yan tawayen Anti-Balaka na Afrika ta Tsakiya Maxime Mokom. REUTERS - PIROSCHKA VAN DE WOUW
Talla

Mai Shigar da Kara na Kotun ICC, Karim Khan ya ce, ofishinsa ya yanke shawarar watsar da duk wani batu na yiwuwar samun Mokom da aikata wani laifi, ko da kuwa an tabbatar da tuhume-tuhumen da ake yi masa. 

Mokom ya fuskanci tuhume-tuhume kan aikata laifukan yaki da kuma cin zarafin bil’adama musamman kan al’ummar Musulmi fararen hula a Jamhuriyar Tsakiyar Afrika a shekarar 2013 da 2014. 

Kasar ta Afrika ta Tsakiya wadda daya ce daga cikin jerin kasashen duniya mafiya fama da talauci, ta tsunduma cikin mummunan rikicin bangaranci bayan ‘yan tawayen Seleka da akasarinsu Musulmai, sun hambarar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Francois Bozize a farkon shekarar 2013. 

Wannan ne ya sa Mokom ya jagoranci kafa Kungiyar Anti-Balaka da zummar karbe iko da babban birnin Bangui daga hannun ‘yan Kungiyar Seleka. 

Mokom ya musanta hannu a zubar da jinin da aka yi, yana mai shaida wa kotun ICC cewa, babban manufarsa ita ce samar da zaman lafiya. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.