Amurka ta dakatar da baiwa Gabon tallafin kudade
Gwamnatin Amurka ta dakatar da da baiwa Gabon duk wasu tallafin kudade, a ci gaba da daukar mataki kan sojojin kasar da suka yi juyin mulki a watan da ya gabata.
Wallafawa ranar:
Sakataren harkokin wajen Amurka Antoni Blinken wanda ke bayar da wannan sanarwa, ya ce babu wani dalili da zai sa Amurka ta ci gaba a baiwa kasar tallafin kudade karkashin gwamnatin soji.
Sai dai sanarwar ta Antoni Blinken ba ta fayyace fannonin da za a dakatar da baiwa kudin ko kuma adadin kudin da za a daina bayarwa ba.
Gabon ita ce kasa ta biyu da aka yi juyin mulki a nahiyar Afrika cikin watanni biyu kachal.
Dakatar da bai wa kasashen da aka yi juyin mulki tallafin kudade ba wani sabon abu bane a Amurka, wadda ke zama tamkar madubin dubawar kasahen da ke takama da dimokradiyya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu