Isa ga babban shafi

Faransa ta dakatar da shirin hadin gwiwar soji da sabuwar gwamnatin Gabon

Ministan Sojin Faransa Sebastien Lecornu ya ce gwamnatin Paris ta dakatar da hadin gwiwar soji da sabuwar gwamnatin Gabon.

Kanar Ulrich Manfoumbi, kakakin kwamitin mika mulki, yana karanta wata sanarwa ta gidan talabijin din kasar.
Kanar Ulrich Manfoumbi, kakakin kwamitin mika mulki, yana karanta wata sanarwa ta gidan talabijin din kasar. AFP - -
Talla

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban kasar Janar Brice Oligui Nguema ya sha alwashin cewa hukumomin kasar za su zama masu bin tafarkin dimokuradiyya, kwanaki biyu bayan juyin mulkin da ya kawo karshen mulkin shekaru 55 na iyalan Bongo.

Kasar dai na da sojoji kusan 400 a Gabon da ke horar da sojojin kasar.

Faransa ta yi Allah-wadai da juyin mulkin da aka yi a Gabon a ranar Laraba, ta kuma jaddada aniyar ta na ganin an mutunta sakamakon da aka samu na zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar Asabar din da ta gabata a kasar da ke yammacin Afirka.

Kasashe biyar ne da nahiyar Afirka da suka hada da Mali Guinea Sudan Burkina Faso da Nijar suka fuskanci juyin mulki cikin shekaru uku da suka gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.