Isa ga babban shafi

Kungiyar Tsakiyar Afrika ta kori Gabon daga cikin mambobinta

Kungiyar Kasashen Tsakiyar Afrika ECCAS, ta dakatar Gabon daga cikin mambobinta, mako guda bayan juyin mulkin soji a kasar. 

Shugaban mulkin sojin Gabon, Brice Oligui Nguema
Shugaban mulkin sojin Gabon, Brice Oligui Nguema AFP - -
Talla

Shugabannin Kungiyar Kasashen Tsakiyar Afrikan ne suka sanar da daukar matakin a kan Gabon biyo bayan wani taro na musamman da suka gudanar a Equitorial Guinea da ke makotaka da ita, inda suka tattauna muhimman batutuwan da suka shafi harkokin siyasa da tsaro a Gabon. 

Yayin zantawarsa da manema labarai, Ministan Harkokin Wajen Angola, Tete Antonio, ya ce shugabannin sun yi tir da yin amfani da karfi wajen kwace mulkin Gabon da sunan samar da mafita a siyasar kasar. 

Shugabannin sun kuma umurci a gaggauta dauke shalkwatar kungiyar da ke babban birnin kasar Libreville, zuwa babban birnin Equatorial Guinea wato Malabo, kana suka bada wa’adi na shekara guda kafin tsara sabon zaben da zai ba su damar tsayar da wanda zai ja ragamar kungiyar. 

Tun a watan Fabairun da ya gabata ne Ali Bongo ya karbi jagorancin Kungiyar Kasashen Tsakiyar Afrika na shekara daya kamar yadda aka saba rarrabawa tsakanin shugabannin, sai dai bayan taron ranar Litinin shugaban Equatorial Guinea, Teodoro Obiang Nguema Mbasogo da ya kasance mataimakinsa ya maye gurbinsa. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.