Isa ga babban shafi

An kama magajin garin Darna gameda ambaliyar ruwan da ta faru a Libya

Jami’an tsaro a Libya sun chafke magajin garin Darna na arewacin kasar da karin wasu jami’ai 7 bisa zargin su da sakacin da ya haddasa mummunar ambaliyar ruwan da ta kashe  mutane fiye da dubu 5 a kasar.

Gwamnatin ta ce ya zama wajibi a gudanar da bincike don kwatowa wadanda ambaliyar ta shafa hakkin su.
Gwamnatin ta ce ya zama wajibi a gudanar da bincike don kwatowa wadanda ambaliyar ta shafa hakkin su. © AFP
Talla

Ofishin Antoni janar na kasar ya ce tuni ya baiwa jami’an tsaro izinin ci gaba da rike mutanen har sai an kammala binciken da ake yi akansu.

Ana dai zargin mutanen da sakaci wajen kulawa da manyan madastun ruwan yankin duga biyu tsahon shekaru, dalilin da ya sa suka balle, al’amarin da ya haddasa mummunar ambaliyar da kasar bata taba ganin irin ta ba.

Manyan madatsun ruwan yankin biyu sun balle ne ranar 11 ga watan da muke ciki na Satumba, sakamakon mahaukaciyar guguwar Daniel da ta taso daga tekun Meditereian, sai dai kuma duk da haka mahukunta na ganin rashin kulawa da madatsun ruwan ne ya sa suka yi raunin da guguwar ta hankado ruwan da ke cikin su.

Gwamnati da sauran kungiyoyin bada agaji sun ce adadin mutanen da suka mutu a sanadin ambaliyar ya kai dubu 5 zuwa dubu 11, kasancewar har yanzu ana ci gaba da tsintar gawarwakin jama’a, sai kuma fiye da dubu 20 har yanzu babu labarin su.

Bayan kammala binciken dai, za a tuhumi magajin garin da manyan jami’an hukumar kula da albarkatun ruwa ta kasar su 7 da laifin sakaci, wasa da aiki da kuma kisan kai, duk saboda kama su da laifin kin kulawa da madatsun ruwan yadda ya da ce.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.