Isa ga babban shafi

Libya: Mazauna birnin Derna sun yi zanga-zanga bayan ambaliya

Daruruwan masu zanga-zanga ne suka taru a birnin Derna, wanda ambaliyar ruwa ta daidaita a ranar Litinin, inda suke zargin mahukunta da yin sake, bayan ambaliya ta yi musu ta’adi, suka rasa dimbim rayuka da kadarori. 

Dandazon mazauna birnin Derna na kasar Libya da suka gudanar da zanga-zanga. 18/09/23
Dandazon mazauna birnin Derna na kasar Libya da suka gudanar da zanga-zanga. 18/09/23 AFP - HUSSAM AHMED
Talla

Masu zanga-zangar sun taru ne a wajen masallacin birnin, inda suka yi ta rera wakokin kin jinin majalisar dokokin da ke gabashin kasar da shugabanta, Aguilah Saleh, su na mai furta zafafar munanan kalamai a kansa. 

Sun kuma bukaci a bude wani ofishin Majalisar Dinkin Duniya a birnin na Derna, tare da fara sake gina birnin, da kuma biyan diyya ga mazauna yankin, wadanda wannan iftila’in ya shafe su. 

Birnin Derna da ambaliyar Libya yafi muni a can.
Birnin Derna da ambaliyar Libya yafi muni a can. AFP - -

Wasu masu zanga-zangar sun yi tattaki zuwa gidan Magajin Garin birnin, Abdulmonem al-Ghaithi, suka kuma banka wa gidan wuta, kamar yadda hotunan da suka karade shafukan sada zumunta da kafafen yada labaran Libya suka nuna. 

Mummunar ambaliya

A ranar 10 ga watan Satumba ce wasu madatsun ruwa biyu, wadanda tun a shekarar 1998 aka sanar da cewa sun tsage suka   fashe, bayan isar mahaukaciyar guguwar Daniel a gabashin Libya, lamarin da ya haddasa mummmunar ambaliyar da ta lakume rayuka sama da dubu 3, dubbai kuma suka bace bat. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.