Isa ga babban shafi

Red Crescent ta musanta alkaluman MDD kan yawan mamata a ibtila'in Libya

Kungiyar agaji ta Red Crescent a Libya ta musanta alkaluman da Majalisar Dinkin Duniya ta bayar kan cewa adadin mutanen da suka mutu a ambaliyar ruwan kasar ya kai dubu 11 da 300, dai dai lokacin da ake cika mako guda da faruwar ibtila'in kuma har zuwa yanzu ake ci gaba da laluben wasu da suka bace.

Akwai dai sabani kan tattara alkaluman wadanda suka mutu a ibtila'in na Libya.
Akwai dai sabani kan tattara alkaluman wadanda suka mutu a ibtila'in na Libya. REUTERS - ESAM OMRAN AL-FETORI
Talla

Wata sanarwa da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar a yau Lahadi ce ke bayyana cewa alkaluman mutanen da suka mutu a ambaliyar ruwan ta Libya ya kai dubu 11 da 300 bisa kafa hujja da alkaluman kungiyar ta Red Crescent, sai dai jim kadan bayan fitar alkaluman Majalisar, kungiyar ta fitar da sanarwar gaggawa da ke nesanta kanta da alkaluman.

Kakakin kungiyar ta Red Crescent a Libyan Tawfik Shoukri ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP daga birnin Benghazi cewa sun kadu matuka da suka ga majalisar ta kafa hujja da su wajen fitar da alkaluman, domin kuwa ko kusa basu bayyana wannan adadi na mutum dubu 11 da 300 a matsayin wadanda suka mutu a Ibtila’in ba.

Sanarwar da Majalisar ta fitar, ta ce baya ga mutane dubu 11 da 300 da suka mutu, akwai kuma wasu dubu 10 da 100 da har yanzu ba a kai ga gano inda suke ba, ko da ya ke har zuwa yanzu gwamnatin gabashin Libya na bayar da alkaluman mutum dubu 3 da 166 ne a matsayin wadanda ibtila’in ya kashe a yankin.

Tuni dai Rasha ta aike da tawagar likitoci ta musamman zuwa Libya don gudanar da aikin dauki a kasar ta arewacin Afrika, dai dai lokacin da wani rahoto na daban ke nuna yadda jami’an agajin Girka 4 suka rasa rayukansu a wani hadarin mota.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.