Isa ga babban shafi

'Yan sanda a Najeriya sun kama jami'ar lafiyar da ta duba mawaki Mohbad

Rundunar ‘yan sandan jihar Legas tare da wasu jami’an lafiya sun tono gawar mawaki, Ilerioluwa Aloba wanda aka fi sani da Mohbad, domin gudanar da bincike kan dalillan da suka haddasa mutuwarsa. 

Dubban mutane ne ke ci gaba da gangami da kunna wuta don nuna girmamawar su ga matashin mawakin na Najeriya
Dubban mutane ne ke ci gaba da gangami da kunna wuta don nuna girmamawar su ga matashin mawakin na Najeriya AP - Nariman El-Mofty
Talla

An dai binne mawakin ne a unduwar Ikorodu da ke birnin Legas kwana guda bayan mutuwarsa a ranar 12 ga watan Satumban nan cikin yanayin da masoyansa ke zargin akwai sa hannu ko tasirin wasu a kan dalilin da ya janyo ajalinsa. 

Ce-ce kucen da mutuwar Mohbad ta haifar ya sanya daruruwan masoyansa gudanar da zanga-zanga kan tituna a jihohin Legas da Ogun da wasu sassan kasar, inda suka bukaci ‘yan sanda su kamo wadanda ake zargi da hannu a mutuwar sa. 

Tun a ranar Litinin da ta gabata, rundunar ‘yan sandan jihar Legas, ta kafa tawagar jami’ai ta musamman da za ta binciki dukkanin hujjoji da kuma wadanda ake tunanin suna da alaka da mutuwar MohBad.

Birnin Lagas a kudancin Najeriya
Birnin Lagas a kudancin Najeriya © AFP/Pius Utomi Ekpei

Mawakin ya fara tashe ne a shekarar 2019 da taimakon Naira Merley, fitaccen mawakin gambara da ke birnin Legas, sai dai mawakan biyu sun rikide zuwa masu hamayya da juna, a shekarar 2022, bayan da shi Mohbad ya bukaci ficewa daga tawagar makawan Naira Marley, amma Marley din ya hana shi sakamakon zargin da ya keyi na cewa Mohbad zai iya tona asirin harkallar miyagun kwayoyi da ake zargin sa da aikatawa.

Tun bayan ballewar ta su ne Mohbad din ke nuna yadda Naira Marley da yaran sa har da abokan arziki ke bibiyar sa don su illata shi,wannan ta sanya wasu ke zargin tsohon Mai Gidan na Mohbad da hannu a mutuwarsa, zargin da yayi watsi da shi. 

Tuni dai 'yan sanda suka sanar da kama jami'ar jinyar da ta duba lafiyar Mohbad din, bayan da ta yi masa wata allura da ake zargin ita ce ta yi ajalin sa da hadin bakin Naira Marley din.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.