Isa ga babban shafi

Adadin waɗanɗa girgizar ƙasa ta kashe a Morocco ya zarta 2000

Adadin mutanen da girgizar kasa mafi muni cikin shekaru da dama ta rutsa da su a kasar Morocco ya haura 2000 yayin da masu aikin ceto ke laluɓen karkashin ɓaraguzai. 

Masu aikin ceto a Morocco na laluben masu numfashi karkashin ɓaraguzai.09/09/22
Masu aikin ceto a Morocco na laluben masu numfashi karkashin ɓaraguzai.09/09/22 AFP - FADEL SENNA
Talla

Girgizar kasa da ba kasafai ake samunta ba, mai karfin gaske ta afku kasar Maroko, inda mutane suka rika tsere daga gadajensu zuwa kan tituna yayin da gine-gine a kauyuka masu tsaunuka da tsoffin garuruwan suka ruguje.

Sama da mutane 2000 suka mutu 

Fiye da mutane 2,000 ne suka mutu kawo yanzu, inda ake sa ran adadin zai karu daidai lokacin da masu aikin ceto ke kokawa don isa yankuna da lamarin ya fi kamari.

Jama'a da dama sun shiga aikin ceto cikin baraguzan gine-gine masu tarihi a birnin Marrakech sakamakon girgizar kasa mai karfin gaske da ta afku a kasar da yammacin ranar Juma'a.

Ƙarfin gaske

Girgizar kasa mai karfin maki 6.8, wadda ita ce mafi girma da ta afku a kasar ta arewacin Afirka cikin shekaru 120, ta sa mutane tserewa daga gidajensu cikin firgici da rashin tabbas da yammacin ranar Juma'a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.