Isa ga babban shafi

Adadin wadanda suka mutu a girgizar kasar Morocco ya zarce 1000

Adadin wadanda suka mutu sakamakon girgizar kasar da ta addabi Morocco ya kai 1037 kamar yadda ma’aikatar cikin gidan kasar ta bayyana a Asabar din nan, inda ta ce akalla mutane 672 de suka jikkata sakamakon wannan iftila’i.

Adadin wadanda suka mutu a girgizar kasar Morocco ya zarce 800.
Adadin wadanda suka mutu a girgizar kasar Morocco ya zarce 800. Al Maghribi Al Youm via REUTERS - AL MAGHRIBI AL YOUM
Talla

Kakkarfar girgizar kasar ta auku ne a cikin daren Juma’a, inda ta lalata gine-gine a kauyukan da ke yankin tsaunukan Atlas, har zuwa birnin Marrakech mai dimbim tarihi.

Girgizar kasar mai karfin maki 6 da digo 8, ita ce mafi karfi da aka taba fuskanta a yankin, kuma mahukunta sun ce akwai yiwuwar adadin mamata ya karu.

Tuni shugabannin kasashen duniya suka fara aikewa da sakwannin nuna goyon baya ga kasar Morocco, biyo bayan wannan al’amari da ya same su, inda a wata sanarwa shugaba  Joe Biden na Amurka ya bayyana alhininsa a game da asarar  rayuka da kadarori da girgizar kasar ta haddasa.

Shi ma shugaban China, Xi Jinping ya aike da sakon ta’azziya ga al’ummar Morocco, yana mai bayyana fatan cewa kasar za ta murmure daga wannan iftila’i da ya  same ta.

Rahotanni sun ce wurin da wannan girgizar kasar ta fi kamari yana da wahalar kutsawa ga masu gudanar da aikin ceto, abin da ke sanya fargabar karuwar adadin wadanda al’amarin ya rutsa da su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.