Isa ga babban shafi

Shugabannin kasashen duniya sun jajanta wa Morocco bayan girgizar kasa

Shugabannin Kasashen duniya da jami’an diflomasiya na ci gaba da aikewa da sakon ta’aziyya da kuma taimako ga kasar Morocco sakamakon kakkarfar girgizar kasar da aka samu a Marrakesh wadda ta yi sanadiyar salwantar rayukan mutane sama da 820.

Wasu masu aikin ceto a wajen inda aka samu girgizar Morocco.
Wasu masu aikin ceto a wajen inda aka samu girgizar Morocco. REUTERS - ABDELHAK BALHAKI
Talla

Daga cikin wadanda suka aike da sakon alhini har da Fafaroma Francis wanda ya mika sakon sa a madadin mabiyansa, yayin da shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bayyana kaduwa da iftila’in, tare da sanar da shugabannin Morocco cewar Faransa za ta taimaka musu wajen kai kayan agaji.

Shi ma Firaministan, Spain Pedro Sanchez wanda ke makotaka da Morocco, ya bayana sakon ta’aziyarsa da kuma taimako ga hukumomin Morocco sakamakon wannan iftila’in, yayin da ya ce zuciyar jama’ar kasar sa na tare da wadanda hadarin ya ritsa da su.

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz da Firaministan Italia Giorgia Meloni duk sun aike da irin wannan sako ga hukumomin na Morocco tare da alkawarin taimaka wa kasar, kamar yadda shugaban majalisar gudanarwar Turai Charles Michel da shugaban kasar Switzerland Alain Berset suka gabatar.

Shi ma shugaban kasar Rasha Vladimir Putin da makocinsa na Ukraine, Volodymyr Zelensky duk sun aike da sakon jaje ga Morocco da kuma tayin kai dauki ga kasar, kamar yadda Firaministan India Narendra Modi da shugaban kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan suka yi.

Ita ma kasar Aljeriya da ta katse hulda da Morocco tun daga shekarar 2021 ta aike da sakon alhini ga jama’ar kasar, yayin da Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya umarci daukacin hukumomin gwamnatin kasarsa da kuma jami’an tsaro da su bai wa Morocco duk irin taimakon da take bukata.

Shugaban Daular Larabawa Sheikh Mohammed bin Zayed Al-Nahyan ya bada umarnin samar da yanayin da za’a gaggauta kai dauki ga jama’ar Morocco da suka shiga cikin mummunar yanayi, yayin da Firaministan Iraqi Mohammed Shia al-Sudani ya ce kasarsa a shirye ta ke ta bada kowacce irin gudumawa domin taimaka wa jama’ar da suka fada cikin wannan iftila’i.

Shi ma Sarki Abdallah na Jordan ya bada irin wannan umarni ga hukumomin kasarsa da su kai wa Moroccon dauki, yayin da Iran ta aike da sakon ta’aziyar ta.

Su ma shugabannin hukumomin duniya sun aike da irin wannan sakon alhini ga jama’a da kuma gwamnatin Morocco domin jajanta musu da kuma gabatar da ta’aziya.

Daga cikin wadanda suka gabatar da irin wadannan sakonni akwai shugaban gudanarwar kungiyar kasashen Afirka, Moussa Faki Mahamat da Sakatare Janar na kungiyar kasashen Musulmi, Hissein Brahim Taha da shugaban hukumar lafiya ta duniya, Tedros Adhanom Gebreyesus da shugaban kungiyar agaji ta Red Cross Jagan Chapagain.

Wadannan shugabanni duk sun bayyana aniyar taimaka wa kasar tinkarar wannan iftila’i.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.