Isa ga babban shafi

Mummunar girgizar kasa ta kashe akalla mutum 300 a Morocco

Ma'aikatar harkokin cikin gida baiyana cewa wata girgizar kasa  mai karfin maki 7.0 da ta lalata yankuna da dama na kasar ta Morocco tare da kashe mutane sama da 300 wasu da dama kuma suka jikkata.

rushewar gine-gine a lokacin girgizar kasa
rushewar gine-gine a lokacin girgizar kasa via REUTERS - AL OULA TV
Talla

Gidan talbijin na Moroko, wanda ya ambato ma'aikatar harkokin cikin gida ta kasar tana bayyana haka, ya kara da cewa mutum 329 ne suka jikkata sakamakon girgizar kasar mai karfin maki 7.0 da ta kassara yankuna da dama na kasar.

Tun da farko wata sanarwa da ma'aikatar cikin gida ta kasar ta fitar da sanyin safiyar Asabar ta ce sama da mutum 300 ne suka mutu yayin da mutane da dama suka jikkata.

Girigizar kasar ta kuma lalata gine-gine yayin da mutane suka rika tserewa daga gidajensu cikin tashin hankali.

Wasu bidiyoyi da aka rika watsawa a shafukan sada zumunta wadanda ba a tantance sahihancinsu ba sun nuna yadda gine-gine suka rika rushewa yayin da wasu suke girgiza. An ga mutane cikin dimuwa yayin da wasu suke fitowa daga baraguzan gine-gine.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.