Isa ga babban shafi

Sojojin Eritiriya sun aikata laifukan yaki a Tigray - Amnesty International

Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International ta ce sojojin Eritiriya da ke kawance da gwamnatin Habasha sun aikata laifukan yaki da cin zarafin bil'adama a yankin Tigray, tare da yi wa fararen hula fyade, bautarwa da kuma kisa na tsawon watanni bayan rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya.

Ana zargin sojojin Eritria da aikata laifukan yaki a yankin Tigray.
Ana zargin sojojin Eritria da aikata laifukan yaki a yankin Tigray. Associated Press
Talla

Kasar da aka yi wa lakabi da “Koriya ta Arewa ta Afirka, Amurka ta sanya mata takunkumi a shekarar 2021, bayan da ta tura dakaru zuwa yankin Tigray domin nuna goyon baya ga dakarun gwamnatin Habasha, tare da zargin sojojinta da laifin kisa, fyade da kuma kwace a yakin shekaru cikin biyu.

Yarjejeniyar da aka kulla a watan Nuwamban shekarar 2022 tsakanin gwamnatin Habasha da 'yan tawayen Tigray ta bukaci janye sojojin kasashen waje daga yankin.

Sai dai Eritrea ba ta cikin yarjejeniyar kuma dakarunta sun ci gaba da kasancewa a yankunan kan iyaka, a cewar mazauna yankin.

Duk da rattaba hannu kan yarjejeniyar tsagaita wuta, an ci gaba da cin zarafin fararen hula a yankin Tigray inda sojojin Eritriya suka ci zarafin mata da suka hada da fyade da kuma bautar da su, yayin da aka kashe fararen hula ba bisa ka'ida ba," in ji Tigere Chagutah, daraktan kungiyar Amnesty a Gabas da Kudancin Afirka.

An yi wa wasu mata fyade a cikin sansanin sojojin Eritrea yayin da aka kai wa wasu hari tare da tsare su a gidajensu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.