Isa ga babban shafi

Eritrea ta koma cikin IGAD bayan shafe shekaru 16 a matsayin saniyar ware

Eritrea ta koma cikin kungiyar hadin kan kasashen gabashin Afirka wato IGAD, bayan shafe kusan shekaru 16 a matsayin saniyar ware a tsakanin kasashen yankin.

Shugaban kasar Eritrea Isais Afwerki.
Shugaban kasar Eritrea Isais Afwerki. REUTERS - MONICAH MWANGI
Talla

A shekarar 2007 gwamnatin kasar ta Eritrea ta dakatar da zamanta mamba a kungiyar ta IGAD, bayan sabanin da ta samu da sauran manbobin kungiyar akan lamurra da dama, ciki kuwa har da kokarin warware rikicin kan iyaka tsakaninta da Habasha, kasar da ta balle daga cikinta a shekarar 1993.

A shekara ta 2021 Amurka ta kakaba wa Eritrea takunkumi bayan da ta tura dakaru zuwa yankin Tigray da ke arewacin Habasha domin marawa sojojin Habasha baya, sai kuma zargin da ake yi wa dakarunta na kashe daruruwan fararen hula a yakin na Tigray.

Eritrea da ke karkashin jagorancin Isias Afwerki tun bayan samun ‘yancin kai daga Habasha shekarar 1993, ta shafe tsawon shekaru 2 tana yakin kan iyaka da tsohuwar uwargijiyarta daga shekarar 1998 zuwa 2000, kafin sulhun da aka yi.

A shekarar 2018 Eritrea ta kawo karshen rikicin da ke tsakaninta da Habasha, ta kuma gayara alakarta da kasashen Somalia da Djibouti.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.