Isa ga babban shafi
China-Eritrea

China ta soki sabbin takunkuman da Amurka ta sanyawa Eritrea

China ta bayyana rashin goyon bayanta ga sabbin takunkuman karya tattalin arzikin da Amurka ta kakabawa Eritrea inda ministan wajen kasar ta Sin Wang Yi ke bayyana cikakken goyon bayansu ga kasar ta gabashin Afrika.

Ministan harkokin wajen China, Wang Yi a ziyararsa zuwa kasashen Afrika.
Ministan harkokin wajen China, Wang Yi a ziyararsa zuwa kasashen Afrika. ANGELOS TZORTZINIS AFP
Talla

A cikin shekarar da ta gabata ne Amurka ta kirbawa Eritrea takunkumin karairaya tattalin arzikin Eritrea saboda  rikicinta da makwabciyarta Habasha.

Dakarun Habasha da na Eritrea an yi ta zarginsu da ayyukan ashsha da suka hada da fyade, kisan fararen bayin Allah haka siddin a yankin Tigray da ake tafka yaki, kuma Amurka.

Ministan waje na China Wang Yi ya gana da Shugaba Isaias Afwerki da Ministan waje Osman Saleh, a jiya Laraba, a ziyarar da yakeyi kasashen na Africa 4, inda suka jaddada muhimmancin zaman lafiya, kare hakkin bil-adama, ‘yancin democradiya da ganin ba’a katsalandan cikin harkokin cikin gid ana duk wata kasa.

Daga Eritrea kai tsaye Wang Yi ya mika zuwa ga kasashen Kenya da tsibirin Comoros a ziyarar da yake yanzu haka a kasashen na Afrika don karfafa alakar da ke tsakaninsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.