Dakarun Somalia na boye sun bayyana a Eritrea
Dakarun Somalia dake karbar horon aikin soji a Eritrea sun fito bainar jama’a a karon farko, shekaru uku bayan da aka fara cece-kuce game da daukarsu aiki.
Wallafawa ranar:
Hoton farko na sojojin Somalian da ya bayyana, yana nuna su ne yayin faretin da suka yi a ranar Asabar, yayin karbar bakuncin sabon shugaban kasarsu Hassan Sheikh Mohamud, wanda ke ziyarar kwanaki hudu a Eritrea.
Mohamud ya ziraci sabbin dakarun nasa ne tare da takwaransa ba Eritea Isias Afawerki a birnin Asmara domin tattaunawa da takwaransa.
Bayanai sun ce tsohon shugaban kasar Somalia Muhd Abdul Farmajo ne ya dauki dakarun kimanin dubu 5 tare da tura su Eritrea don samun horo.
Sai dai matakin ya zamewa tsohon shugaba Farmajo kadangaren bakin tulu, bayan da 'yan adawa suka rika caccaka tare da nanata iyaye suna kokawa da cewa 'ya'yansu sun bace.
Daga bisani ne kuma Iyayen sabbin sojojin Somalian da aka tura karbar horon suka gudanar da zanga-zanga a birnin Mogadishu inda suka ce gwamnati ta yaudare. su ne da cewar za ta tura ‘ya’yan nasu aiki ne a kasar Qatar, sai kuma kwatsam suka bayyana a kasar Eritrea, inda aka tura su karbar horon soji ba tare da son ransu ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu