Isa ga babban shafi
Somalia

An kafa sabuwar rundunar kawar da ta'addanci a Somalia

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya kada kuri’ar amincewa da sabuwar rundunar wanzar da zaman lafiya a Somalia, kasar da kungiyar Al-Shebab ta shafe sama da shekaru 10 tana fafutukar kifar da gwamnati.

Rundunar AMISOM mai yaki da 'yan ta'adda a Somalia
Rundunar AMISOM mai yaki da 'yan ta'adda a Somalia Reuters/Feisal Omar
Talla

Rundunar Wanzar da Zaman Lafiya ta AMISOM wadda a yanzu take aiki a Somalia, na kunshe da jumullar sojoji dubu 20 da jami’an ‘yan sanda da wasu fararen hula masu taimaka wa kananan hukumomi wajen yaki da mayakan jihadi a kasar.

A wannan Alhamis din ne, aikin wannan rundunar ke kawo karshe a kasar ta Somalia, yayin da Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres ya bada shawarar ci gaba da wanzuwar rundunar har zuwa karshen shekarar da muke ciki.

Kwamitin Sulhun ya tsayar da kudirin sake fasalta wannan rundunar ta AMISOM, inda a yanzu ake yi mata lakabi da ATMIS.

Sabuwar rundunar ta ATMIS za ta yi aiki domin agaza wa sojojin Somalia wajen gudanar da aikinsu na samar da tsaro a matakin farko.

Kudirin  Kwamitin Sulhun dai, ya amince cewa, sannu a hankali, za a janye rundunar a zango-zango hudu har zuwa lokacin da za a kammala janyewar a karshen shekarar 2024.

Kasar Somalia wadda ke yankin kahon Afrika, ta fuskanci jerin hare-hare a ‘yan makwannin nan a daidai lokacin da take kwan-gaba-kwan-baya dangane da shirya zaben shugaban kasa da aka sha jinkirtawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.