Isa ga babban shafi

'Yan ta'adda dama sun mutu yayin arangama a tsakiyar Somalia

Sojojin gwamnati 3 da ‘yan ta’adda masu ikirarin jihadi da dama ne suka mutu a wata gwabzawa da aka shafe sa’a guda ana yi, bayan wani hari da ‘yan ta’addan suka kai garin Baxdo da ke tsakiyar kasar Somalia, kamar yadda wani kwamandan soji ya bayyana.

Dakarun Somalia sun tsawon sa'a guda suna gwabzawa da 'yan ta'adda da suka kawo musu hari.
Dakarun Somalia sun tsawon sa'a guda suna gwabzawa da 'yan ta'adda da suka kawo musu hari. REUTERS - FEISAL OMAR
Talla

Wannan lamari na nuni da daya daga cikin dimbim kalubalen da sabon sabon zababbaen shugaban kasar ke daf da tinkara.

Mayakan kungiyar Al-Shabaab masu dauke da muggan makamai ne suka kai wanna hari, da sanyi safiyar Lahadi.

Sai da suka  tarwatsa wata mota makare da bam kafin su warwatsu zuwa yankunan garin Baxdo, mai nisan kilomita 600 daga arewacin babban birnin kasar, Mogadishu.

Kamfanin dillancin labaran Faransa ya ruwaito wani ganau yana cewa ya ga gawarwakin ‘yan ta’adda 13 a inda aka yi gumurzun.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.