Isa ga babban shafi

Fararen hula sun soki yarjejeniyar tilista wa 'yan ci rani a Turai

A cikin wata makala da kafofin yada labaran kasashen Tunisia da Faransa da Italiya suka yada,  masana da wakilan kungiyoyin farar hula na kasashen kudanci da arewaci, sun ja daga kan salon siyasar  kasashen Turai da Tunisia ta kin jinin baki 'yan ci rani.

yan ci ranin kasshen Afrika bakar fata a kan iyakar da ta hada Libiya da Tunisia. alhamis  4 ga watan Ogustan  2023.
yan ci ranin kasshen Afrika bakar fata a kan iyakar da ta hada Libiya da Tunisia. alhamis 4 ga watan Ogustan 2023. © Yousef Murad / AP
Talla

Gomman mutanen da suka rattaba hannu kan makalar da suka fito daga kasshen Faransa da Tunisia da Libya da Italiya da  Jamus da Algeria da Nijar da Amurka da kuma Canada ne, a dunkule suka soki tsarin yarjejeniyar fahimtar juna kan huldar tsaro tsakanin Kungiyar Tarayyar Turai da kasar Tunisia da suka  saka wa hannu a ranar 16 ga watan Yulin 2023.

Ita dai wannan makala da masanan da suka kasance malaman jami’a da alkalai da mambobin kungiyoyi masu zaman kansu, an yada ta ne a shafukan jaridun  kasar Italiya da kuma kan shafin yada labarai na kasar Faransa  Mediapart  da kuma jaridar Nawaat ta kasar Tunisia.

Makalar ta nuna takaicinta kan yadda  kasar T unisia ta fito fili ta shimfida salon siyasar tursasawa, kora  da kuma tsangwar yanci ranin asalin kasshen nahiyar Afrika bakar fata.

Mawuyacin hali ne baki matafiya ci rani ke ciki a kasar Tunisa tun bayan lokacin da shugaban kasar Kais Saied, da awatan yulin 2021 da ya karawa kansa karfin iko, a ranar 21 ga watan fabarairun wannan shekara ne ya bayyana rashin kaunarsa ga yanci ranin, da yake zargin cewa kasancewarsu a kasarsa zai sauya tsarin zaman al’umma a kasar ta Tnisiya.

Sakamakon wata taho mu gama da ta yi sanadiyar rasa ran wani dan Tunisa a ranar 3 ga watan yulin da ya gabata, daruruwan yan ci ranin kasashen Afrika bakar fata ne aka kora daga garin Sfax  gari na biyu mafi girma a kasar Tunisia, inda mahukumta suka tisa keyarsu, a cikin rairayin hamada a wani guri dake kusa da kan iyakokin kasashen  Libya da  Algéria, ba tare da ruwa ko abinci balantana malaba a cikin tsananin zafin da ya zarta maki 40 da dama ne daga cikin yan ci ranin suka rasa rayukansu a cewar kungiyar kare hakkin dan adam ta Human Rights Watch.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.