Isa ga babban shafi

HRW ta zargi hukumomin Tunisiya da cin zarafin bakin haure

Wani sabon bincike da kungiyar kare hakkin bil'adama ta Human Rights Watch ta gudanar, ya gano cewa jami'an tsaron kasar Tunusiya na cin zarafi ga bakin haure 'yan Afirka bakar fata, inda kungiyar ta yi kira ga kungiyar Tarayyar Turai da ta dakatar da tallafin da take baiwa kasar.

Wasu bakin haure bakar fata kenan, da suka taru a wurin shakatawa na Sfax da ke kasar Tunisia
Wasu bakin haure bakar fata kenan, da suka taru a wurin shakatawa na Sfax da ke kasar Tunisia REUTERS - JIHED ABIDELLAOUI
Talla

Cin zarafi da Human Rights Watch ta gano ana tafkawa kan baki sun hada da duka, amfani da karfi fiye da kima, wasu lokuta har da azabtarwa, kamawa da tsare su ba bisa ka'ida ba, korar jama'a, korar tilas, da satar musu kudi da kayayyaki.

Tun farkon wannan shekara ne kasar Tunisia fara fama da matsalolin bakin haure.

Babban jami’in sashen bincike da kare hakkin ‘yan gudun hijira na Human Rights Watch, Lauren Seibert ya ce hukumomin Tunisiya sun ci zarafin baki bakaken fata, suna kara rura wutar nuna wariyar launin fata da kyamar baki, tare da mayar da mutanen da suka gudu a cikin kwale-kwale da ke fuskantar barazana, inda suka fito ba tare da la’akari da kalubalen da za su fuskanta ba.

A watan Maris ne, kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch ta gudanar da hira ta wayar tarho da mutane 24, da suka hada da maza 22, da mace daya, da yarinya daya da ke zaune a Tunisia.

Daga cikin su akwai bakin haure 19, da masu neman mafaka guda hudu, da kuma dan gudun hijira daya, da suka fito daga kasashen Senegal, Mali, Cote d’Ivoire, Guinea, Saliyo, Kamaru, da Sudan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.