Isa ga babban shafi

kungiyar agaji ta Red Cross ta ceto baki 630 a Tunisia

A kasar Tunisia, kungiyar agaji ta Red Cross ta ceto kusan bakin haure 600 da suka hada da yara a kan iyakar ta da kasashen Tunisia da Libya. Bakin haure da dama ne suka tsera daga kasar ta Tunisia tun bayan barkewar rikici a ranar 3 ga watan Yuli inda wani 'dan kasar Tunisia guda ya mutu, yayin da wasu dama daga cikin su suka makale a kan iyakar kasar  da Libya. 

Wasu daga cikin bakin haure a yankin Sfax na kasar Tunisia
Wasu daga cikin bakin haure a yankin Sfax na kasar Tunisia © AFP / HOUSSEM ZOUARI
Talla

Abdellatif Chabou, shugaban kungiyar ta Red Cross a kasar ta Tunisia ya bayyana cewa bakin haure sun fuskanci karancin abinci da ruwan sha. 

Wasu bayyanai daga shugaban wannan kungiya sun ce adadin ka iya karuwa nan da zuwa wani lokaci muddin gwamnatocin kasashe ba su dauki matakan da suka dace na bayar da kulawar da ta dace ga bakin ba.

Wasu daga cikin bakin haure da aka kai kan iyaka da kasar Tuunisia
Wasu daga cikin bakin haure da aka kai kan iyaka da kasar Tuunisia AP

Wani 'dan jarida na kamfanin dilancin labaran Faransa na AFP ya dauki hotuna da bidiyo inda ake hango yara kanana a wata makaranta da ke Ben Guerdane mai nisan kilomita 40 a gabashin Ras Jedir. 

'Dan jaridar ya kara da cewa an kai wata tawagar ta bakin haure  Medinine da Tatouine dake kudancin kasar. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.