Isa ga babban shafi

'Yan sandan Tunisia sun tarwatsa bakaken fata a kasar

'Yan sandan Tunisia sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa bakin-haure bakar fata, wadanda suka shafe kwanaki suna gudanar da zanga-zanga a wajen ofishin Majalisar Dinkin Duniya domin neman a kwashe su daga kasar. 

Jami'an 'yan sandan Tunisia
Jami'an 'yan sandan Tunisia AFP - FETHI BELAID
Talla

Yayin Karin bayani kan yadda lamarin ya auku, wakilan kamfanin dillancin labarai na AFP sun ce akan idanunsu 'yan sandan Tunisia suka tarwatsa sansanin wucin gadin da bakin-hauren suka kafa a wajen ofishin hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya da ke birnin Tunis. 

A farkon watan nan ne dai hukumar ta UNHCR ta dakatar da ayyukan ba da mafaka a dukkanin ofisoshinta da ke sassan duniya har sai ta kammala komawa kan sabon tsarin yi wa bakin-hauren rijista. 

Famoussa Koita, wani dan kasar Mali da yake da rijistar zama halastaccen mai neman mafaka, ya ce abokan zamansa da dama a kasar ta Tunisia sun shafe shekaru biyu zuwa uku suna neman a yi musu rijista ba tare da samun nasarar hakan ba. 

Wasu daga cikin bakin-haure bakaken fata a Tunisia
Wasu daga cikin bakin-haure bakaken fata a Tunisia AP - Hassene Dridi

Shi kuwa kakakin ma'aikatar harkokin cikin gidan Tunisia Faker Bouzghaya ya ce 'yan sanda sun tarwatsa zanga-zangar bakin-hauren ne a bisa bukatar hukumar ta UNHCR, kuma kawo yanzu an tsare 80 daga cikinsu. 

Daruruwan bakin-haure bakar fata sun shafe makwanni a wajen  harabar ofishin Hukumar Kula da ‘yan gudun Hijira ta Duniya a birnin Tunis, ba tare da bandaki ko ruwan sha mai tsafta ba, tun bayan da a watan Fabarairu shugaban Tunisia Kais Saied ya yi ikirarin cewa bakin akasarinsu daga yankin kudu da Sahara miyagu  ne da suke neman sauya  asalin kasarsa, lamarin da ya janyo musu fuskantar cin zarafi, baya ga kora daga gidajen da suke zaune da kuma wuraren ayyukansu, saboda tsoron biyan tara ko kuma shan dauri a gidan yari. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.