Mutane 34 sun mutu a hatsarin mota a Aljeriya
Akalla mutane 34 ne suka mutu yayin da 12 suka jikkata a jiya Laraba a wani karon tawo mu gama tsakanin motoci guda kusa da Tamanrasset, a kudu mai nisa na Aljeriya.
Wallafawa ranar:
Hatsarin wanda ya biyo bayan gobarar ya afku ne a lokacin da motar bas da ta hada Adrar zuwa Tamanrasset mai tazarar kilomita 2000 daga babban birnin kasar Algiers ta afkawa wata motar kasuwanci.
Yawancin wadanda harin ya rutsa da su sun kone kurmus, kamar yadda kafafen yada labaran kasar suka bayyana.
Gudun masu ababen hawa ciki har da direbobin motocin jama'a ne ke haddasa hadurran kan tituna a kasar Aljeriya, a cewar hukumar kula da hadura ta kasar da aka sani da National Safety.
A cikin shekarar 2022, Aljeriya ta sami kusan hadurran 22,980 na ababen hawa, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 3,409 da raunata 30,479, a cewar wakilin kiyaye hadura a kan hanyoyin mota na kasa, Nacef Abdelhakim.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu