Isa ga babban shafi

Lokaci ya yi da Africa zata takawa turawa birki kan tilasta mata karbar auren jinsi-Ebrahim Raisi

Shugaban kasar Iran Ebrahim Raisi ya soki kasashen yammacin duniya bisa yadda suke kokarin kakabawa kasashe akidar auren jinsi kan dole.

Le président iranien Ebrahim Raïssi le 4 novembre 2022 à Téhéran.
Le président iranien Ebrahim Raïssi le 4 novembre 2022 à Téhéran. AP - Vahid Salemi
Talla

A ci gaba da ziyarar da yake yi wasu daga cikin kasashen Nahiyar Africa don karfafa alakar da ke tsakanin Iran da Africa, Raisi ya ce, lokaci ya yi da ya kamata kasashen Africa su fara takawa turawa birki, game da shigar musu da munanan dabi’u da suka yi hannun riga da al’adu da kuma addinan su.

Yayin ganawar sa da shugaban Uganda Yuweri Museveni a birnin Kamfala fadar gwamnatin kasar, Raisi ya yabawa gwamnatin kasar dama ‘yan Majalisa bisa yadda suka jajirce, wajen hana masu dabi’ar auren jinsi samun wajen zama a kasar.

Shugaba Ebrahim, ya ce matukar duniya ta rungumi wannan dabi’a ta auren jinsi, nan ba da jimawa ba, yawan jama’a a duniya zai ragu matuka, wanda hakan kuma illace, musamman ga Nahiyar Africa da jama’ar ta suka saba da auratayya da kuma tara zuri’a.

Ko da yake batu kan harkokin diplomasiyya, shugaban na Iran, yace dama can akwai dadidiyyar kyakyawar alaka tsakanin Iran da Uganda, don haka ne ya je kasar a yanzu domin farfadowa da kuma karfafa ta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.