Isa ga babban shafi

Kotu ta bada umarnin sakin 'yar adawar da ta kwashe watanni 4 a tsare aTunisia

Alkali a Tunisiya ta bada umarnin sakin daya daga cikin mayan ‘yan adawar kasar Chima Issa, bayan da ake tsare da ita tsawon watanni hudu, bisa zarginta da shirya kutungwila ga sha’anin tsaron kasar, kamar yadda lauyan ta ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP.

'Yan Tunusiya a lokacin da suke zanga-zanagar adawa da shugaban kasar  Kais Saied.
'Yan Tunusiya a lokacin da suke zanga-zanagar adawa da shugaban kasar Kais Saied. AP - Hassene Dridi
Talla

Lauyan da ke kare ta Dalila Msaddek ya ce da wannan hukuncin, Chima Issa za shaki iskar ‘yanci har sai idan masu gabatar da kara sun daukaka kara don kalubalantar hukuncin da alkalin da ke sashin yaki da ta'addanci ya yanke.

Chima wacce jigoce a jam’iyar NSF, a watan Fabarairun da ya kagaba ne aka kamata ta re da wasu ‘yan adawa da ma’aikatan kafafen yada labarai da ‘yan kasuwa 20.

Ana dai tuhumar su ne da kokarin yiwa tsarin tsaron kasar zagon kasa, duk da cewa shugaban kasar Kais Saied ya ayyanasu a matsayin ‘yan ta’adda.

Tun bayan rushe majasar dokokin kasar da kuma kokarin gurgunta sha’anin dimukaradiyarta da shugaban ya yi, ya fara fuskantar suka daga bangarori daban-daban.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.