Dubban mutane sun yi gangamin goyawa shugaban Tunisiya Kais Saied baya
Dubban magoya bayan shugaban Tunisiya Kais Saied sun yi gangami a babban birnin kasar da wasu biranen a wannan Lahadi don nuna goyon baya ga dakatar da majalisar kasar da kuma yin alkawarin sauya tsarin siyasa, matakin da masu sukar shugaban ke kira juyin mulki.
Wallafawa ranar:
Zanga -zangar akalla mutane dubu 8 a tsakiyar Tunis ita ce mafi girma da aka gani, idan aka kwatanta da fitowar masu adawa da matakin tun lokacin da Saied ya kwace ikon zartarwa a watan Yuli.
A ranar 25 ga watan Yuli, bayan watanni na rashin jituwar siyasa, shugaba Saied ya kori Firanminista, kana ya dakatar da majalisar dokoki sannan ya karawa kansa karfin ikon.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu